23 Yuni 2015 - 14:46
An Cafke shugaban tara bayanan sirri na Rwanda

Jami’an tsaro a birnin London na Birtaniya sun cafke shugaban hukumar tara bayanan sirri ta kasar Rwanda Emmanuel Karenzi Karake a karkashin wani sammacin da kasar Spain ta fitar.

Tun a shekara ta 2008 ne dai wani rahoton bincike ya zargi Emmanuel Karenzi Karake da hannu a aikata kisan kare dangin kasar ta Rwanda wanda ya faru a shekarar 1994, musamman ma kisan wasu ‘yan kasar ta Spain su uku dake aikin jinkai a Rwanda.

Tuni dai ministar harkokin wajen Rwanda, Louise Mushikiwabo ta soki cafke Karake, inda ta ce, ba za su amince da hadin kan da Kasashen yamma ke yi da junansu ba domin musgunawa ‘yan afrika.

Rahotanni na cewa, gwamanatin Kasar ta Rwanda ta bukaci Kasar Birtaniya da ta gabatar mata da bayanai kan yadda aka kama Karenzi da ya wakilci gwamanatin Rwanda a wani aiki da zai dauke shi tsawon mako guda a kasar ta Birtaniya.288